4 Disamba 2018 - 15:11
Nicolas Maduro Na Wata Ziyarar Aiki A Rasha

Nicolas Maduro Shugaban kasar Venezuella,ya soma wata ziyarar aiki a kasar Rasha, inda zai gana da takwaransa Vladimir Putin a birnin Moscow.

A Lokacin ziyarar bangaroron biyu zasu tattauna kan zantuka da dama da suka shafi alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Dama kafin hakan, shugaban Maduro, ya gana da takwaransa na Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, wanda ya kai masa ziyara a birnin Caracas.

Ko a kwanakin da suka gabata ma dai shugaba Maduro, wanda kasarsa ke fuskantar matsin lamba da takunkumin Amurka, ya gana da wata babbar tawaga ta manyan jami'ai daga kasashen Iran da kuma Koriya ta Arewa.

Mista Maduro dai ya danganta mastin lambar Amurka da takunkuminta a matsayin abubuwa dake kara dagula al'amura a duniya.